Angon Da Ya Auri Mata 8 Lokaci Daya Ya Bayyana Irin Wahalar Da Yasha A Daren Farko
Wani ango mai sana’ar zanen Tattoo ɗan ƙasar Thailand ya bayyana cewa yana zaune a gidansa tare da matansa guda takwas duk ’yan mata waɗanda ya aure su kusan lokaci ɗaya labrin da ya dauki hankalin jama’a sosai a Intanet.
Angon mai suna, Ong Dam Sorot, matashi ne mai zanen Tattoo da ya ƙware a zanen gargajiya na ‘yantra’ na asalin addinan Indiya, kwanan nan ya gana da wani sanannen dan wasan ban dariya na ƙasar Thailand don yi hira game da matakin aurensa mai cike da kace- nace.
Ango Sorot, ya auri mata takwas kuma suna zaune a gida ɗaya kuma suna ɗaukar kansu a matsayin iyali guda cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Hirar wadda aka sa a shafin Youtube, kawo yanzu ta samu ra’ayin jama’a sama da miliyan 3 a shafin.
Ong Dam Sorot, ya gabatar da matan nasa ɗaya bayan ɗaya tare da bayyana yadda suka hadu. Matan takwas dai sun nuna mijin nasu a matsayin mai matuƙar kirki, mai kula da al’umma, kuma sun yi ikirarin more rayuwa.