Gwanin Sha’awa Bidiyon Yadda Jaruma Fati KK Suke cin Amarcinsu tare da Sabon Angonta, Allah Ya bada Zaman Lafia
Tsohuwar jarumar Kannywood Fatima Sadisu wacce akafi sani da Fati KK, ta daura wani Sabon Bidiyonta tare da Sabon Angonta a Shafinta na Instagram inda ta kara dayin Addu’ar Allah Yasa mutuwa ce zata raba ta da sabon mijin nata.
An daura auren tsohuwar jarumar ne a ranar Juma’a 9 ga watan February na wannan Shekara ta 2024 da sahibin nata mai suna Hassan Sani Umar da misalin ƙarfe 11 na safe a Layin Mustapha Salihawa dake Sabon Kawo, Kaduna.
Ɗaurin auren ya biyo bayan taƙaitaccen zawarcin da Tsohuwar Jarumar tayi ne tun bayan mutuwar auren ta a Kano Wanda Ya faru a cikin Shekarar 2023.
Bayan daurin Aure Jarumar ta bayyana irin farim cikin ta inda ta wallafa a Shafin ta na Instagram cewa Alhamdulillah, Allah Kasa Mutuwa ce Zata rabani da Mijina alfarmar Annabi (S.A.W) Allah ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali.