News
Kotu ta daure wani lebura saboda ya saci wake kwano bakwai a garin jos
Jaridar Alfijir Hausa ta ruwaito yadda Wata kotu ta yanke ma wani lebura hukuncin ɗaurin wata huɗu a gidan yari, kan satan kwano bakwai na wake.
Dan sanda mai gabatar da ƙara ya shaidawa kotun cewa, dubun matashin mai shekaru 20 tacika ne biyo bayan ya ɓalle shagon mai sayar da hatsi ya sace mishi kwano bakwai na wake da manja, da kiret-kiret na lemu da sauran kayan abinci, sannan ana zargin shi da sace wasu kayan wuta da suka kai kimanin naira 172, 000.
Bayan sauraron kara kotun ta yanke wa saurayin hukunci tare da bashi zabin biyan tarar N30, 000 da kuma wata dabu 30, 000 din ga mai shagon.
“Alƙalin yace, ya yanke hukuncin ne domin ya zamo izina ga masu aikata laifuka irin haka.