News

Matar Shugaba Tinubu Ta Fadi Abinda Ya Kamata A Yiwa Masu Garkuwa Idan An Kamasu

Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa masu garkuwa da mutane a matsorata ne.

Ta kuma nuna cewa duk wanda aka samu da laifin yin garkuwa da mutane ya cancanci hukuncin kisa.

Ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani kan labarin wasu mata 200 da aka yi garkuwa da su a jihar Borno, da kuma dalibai da malamai sama da 280 da aka sace a jihar Kaduna.

Remi Tinubu ta ce, “Duk wanda ke garkuwa da kananan yara to ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa, mugu ne, kuma matsoraci ne.

“Ya isa haka kuma ina kira ga gwamnonin jihohi cewa da zarar an kama su, to a zartar musu da hukuncin kisa.

“Me yasa basa daukar mutane daidai girman su? Me yasa suke azabtar da yaranmu? Abin da suke ƙoƙarin yi shi ne kashe mana rayuwa.

“Dukkanmu mun san iyaye, idan mun tsufa muna dogara ga ‘ya’yanmu ne.

“Me ya sa za ku je ku kwaso su daga makarantu, a yanzu ina ganin ya isa haka, a matsayina na tsohuwar yar majalisa, na yi imanin cewa duk wanda aka kama daga cikinsu ya cancanci kisa.

– Daily Nigerian Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button