News

Wa’iyazubillahi Sabuwar Masifar Data Kunno Kai A Makarantun Boko Abun Ya Munana

Babu shakka yana da kyau, idan ka kammala karatu ka nuna godiya ga Allah da kuma iyaye da suka baka gudummawa har ka kai ga cimma burinka.

Amma sai dai kash matasanmu maza da mata daga sakandire hadi makarantun gaba da sakandire, suna wannan shagulgulane ta yadda suke cakudedeniya i junansu suna aikata ababen da basu dace ba.

Wallahi akwai wata makaranta danasani, a ranar da daliban makarantar za su yi graduation, a ranar wasu daga cikin mazan da matan ke aikata zina, wasu kaga matan da mazan na kusantar wadanda ba muharramansu ba, abin takaici harda mata da mazan aure, kaga mutum na taba Nonon mace da sunan sign out.

Ni Sai nake ganin shiyasa ake ta samun matasa da tarin degree babu albarka, babu aikin Yi, ina amfanin BADI BA RAI.

Yana da kyau hukumomin gwamnati dana makarantu musamman na Arewacin kasar nan,su haramta (signing out) da dalibai marasa tarbiyya suke yi idan sun kammala jarabawar karshe, saboda ya saɓa ma addini da al’adun mutanen Arewa.

Allah ka bamu iKon gane gaskiya mukuma yi amfani da ita.

Irin Abubuwan Da Suke Faruwa A Makarantu
Kun san yadda daliban da suka kammala karatunsu ke yin balaguro yayin da suke yin taron sa hannu bayan sun gama da takardarsu ta ƙarshe a makaranta?

To, waɗannan ɗaliban sun ɗauki daji zuwa wani matakin kuma kamar yadda ake iya gani a fili, sun yi farin ciki sosai da aka yi da makaranta.

Hotunan an yada su a Facebook kuma musamman wadanda aka sanya kirjin mace a hannun samari su ne suka sa mu fahimci irin farin cikin da wadannan daliban ke yi na rashin zuwa makaranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button