News

Wata Kirista ta tsinci kanta a asibiti bayan ta suma sau Biyu kafin karfe 4 na rana daga gwada yin azumin Ramadan

Wata Kirista ta tsinci kanta a asibiti bayan ta suma sau Biyu kafin karfe 4 na rana daga gwada yin azumin Ramadan.

Wata kirista Eniola Fagbemi wacce ke auren wani musulmi a Kudu ta yi kurarin cewa azumin musulmi bashi da wuya tunda suna yin sahur kuma su sha ruwa lokacin magriba, don haka tace za ta jaraba don ta tabbatar masa.

Mahanga ta ruwaito Sai dai bayan Eniola ta yi sahur wajajen 4:30 na asuba tun wajen karfe 12 na rana ta fara fita hayyacinta, kan kace kwabo ta suma sau Biyu wajajen ƙarfe 4 na yamma ba arziki aka kwashe ta sai asibiti.

Allah ya taimaka an ceto rayuwar ta a asibitin Saanu Hospital dake garin Mokola.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button