Yadda Asirin Wasu Maginta Da Suke Lalata Rayuwar Yan Mata Ya Tonu
Ana zargin wasu magidanta guda uku da yima wata matashiyan yarinya wadda shekarunta basu gaza 13 ba a duniya fyade a wani gidan gasa bredi dake garin zariya tudun wada a jihar Kaduna.
A yayin da mahaifiyar kurmar yarinyar ta an kara ta shaida cewa sun kwana biyu suna amfani da yarinyar, Amma bata gane ba sai da aka kwana biyu taga yarinyar yanayinta yana sauyawa.
Malam Mohammad Danliti shine mai unguwar gangaren kwadi ya tabbatarwa jaridan Aminiya faruwan lamarin inda yace bayan da mahaifiyanta ta gano wasu alamun canji a jikinta batayi tunanin cewa wasu ne suka aikata mata hakan ba.
Yace, sai daga baya daya daga cikin kawayen kurma ta sanar da mahaifiyanta cewa tana ganin bebiyan tana yawan zuwa gidan biredin ana bata kuɗi.
A wani bincike da gidan jaridar Aminiya ya gudanar a asibitin Gambo sawaba, inda aka kai yarinyan domin duba lafiyanta wanda likitoci suka tabbara da anyiwa yarinyan fyade kuma harsun saka mata cuta a kan kin ta.